Topic: Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (3)
Timeline: 2012-08-24 02:09:21
A Rubuce Da Malam Ahmad Tijjani Sa’id
Tasirin Ramadan Kan Inganta Tarbiyyar Al’umma (3)
A makon jiya mun fara kawo bangare na biyu na laccar Ramadan da Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi da hadin gwiwar kungiyar dalibai Musulmi ta kasa (MSS) reshen jihar suka shirya a Babban Masallacin Bauchi,. Sai dai saboda gajiyawa irin ta dan Adam mun sake bayyana Malam Abdurrahman Ibrahim Idris a masatyin wanda ya gabatar da laccar ta makon jiya maimakon Mala Ahmad Tijjani Sa’id. Muna fata za a gafarce mu. To yau ga sauran abin da za mu iya gabatarwa daga laccar Malam Ahmad:
Sannnan bayan ka samu halal din nan kada ka rika take cikinka da abinci. Manzon Allah (SAW) ya bayar da shawara kan yadda za a ci abinci. Ya ce: “dan Adam bai taba cika wata jaka da ta zamo masa sharri kamar cikinsa ba.” Domin cikin yana dauke da abubuwan da babu masana’antar da ba ta wadannan abubuwa ta iya dauka saboda yawansu. Mai narka abinci, mai tura shi mai… Allah da Ya halicccin mutum Ya sanya wadannan kayayyaki Ya matse su a cikin wannan jakar har mutum yake iya tafiya da su, Shi ne kawai Ya san abin da ke ciki. Amma idan ba ciki ya girma ya zama tumbi ba, ba ma za ka gane yana nan ba.
Saboda haka ana so ka misaltu da wannan siffa na Annabi (SAW) da ya ba mutum game da cin abinci. ’Yan lomomi kadan sun ishi mutum. An taba tambayar Sheikh Usman dan Fodiyo (RA), cewa mutumin da ya manta bai yi bismillah a lomar farko ba yaya zai yi? Sai ya ce, sai ya yi a ta biyu. Sai aka ce in ya manta a ta biyun fa? Sai ya ce, sai ya yi a ta uku ta karshe. Wato shi a wajensa bai kamata a ce lomomin sun fi uku ba.
Saboda haka ’yan lomomi kadan sun ishi mutum, amma in ya zama, wanda halittarsa sai ya ci da yawa ne fa. Annabi (SAW) mai tarjamar maganar Allah ne, sai ya ce ga shawara. Sai ya kasa cikinsa uku duk cin sa, daya ya sa abinci, daya ya sa abin sha, daya ya bari domin numfashi. Shi ne cikinka zai yi aiki ba tare da wahala ba, domin ko dakin na’ura in babu kayan sanyi za su hade su narke su lalace, abin da ka yi dominsu ba zai biya ba, to haka cikin dan Adam yake. Wannan fa in an sha ruwa ke nan, kada kuma a ce za a take ciki. Domin babbar illar ita ce, sha’awar nan da aka ce mutum ya kame kashi 70 cikin 100 tana ta’allake ne da abincin da mutum yake ci. Ka yi sahur ka take cikinka da abinci, sai wajen karfe 11 da rana zai fara aiki. Kuma cikin abin da zai tayar maka na sha’awa kalle-kalle ne. In ka cika cikinka abin da fara raya maka shi ne tunanin mata. Don haka aka kayyade maka yadda za ka ci abinci, don kada ya narke tunaninka ya tafi, a rasa tarbiyyar da azumi ke koyarwa.
Sannan a cikin madaukan mutum akwai farjinsa. Alal hakika farji halitta ce da Allah Ya yi wa mutum a jikinsa. Son mata dabi’a ce ga mutum ba yadda za a yi ya kauce mata, kullum mutum yana tattare da sha’awa. Azumi mai kyau shi ne rigakafi ga auka wa sha’awa. Duk abin da zai jawo ka ji sha’awar mace ma ka kauce masa, ba sai sha’awar ta zo ka kare kake jarumi ba, ka kauce wa mukaddimatin sha’awar. Sha’awa ta taso ka kare ta jarumta ce ta bayan azumi.
Sannan abu na gaba su ne madaukanmu, in an ce madaukai a takaice su ne hannuwa da kafafu, amma da azumi ana riskar da ido da kunne da hanci duka a cikin madaukai. Hanci zai jawo kanshin da bai kamata ka ji ba, kunne zai jawo kara ku muryar da bai kamata ka ji ba, ido zai hango abubuwan da ba su kamata ka gani ba. In sa jawo maka kuma su za su motsa kafafu su tafi wurin, su motsa hannunwa su taba abin. Saboda haka wadannan abubuwa suna da tasu tarbiyya ta musamman a cikin azumi da ake so a yi musu. Kada su hango abin banza, domin ido yana azumi, Hadisi ne ingantacce. Kunne yana azumi hanci yana azumi. In ka yi azumi ka daina ci da sha, wadannan gababuwa ba su kiyaye nasu bangaren ba, to lallai da wuya azumin nan ya zamo azumi a wurin Allah. Azumi a wurinka daban, azumi a wurin Allah daban. Azumi karbabbe a wurin a wurin Allah, sai ya zamo ka azumtar da wadannan gababu, ba ka kai su inda za su halakar da wannan azumi naka barin ci da sha da saduwa da iyali ba.
Allah Ya halicci mutum Ya san abubuwan da suke tare da shi, don haka ya sanya azumi domin ya gyara tarbiyyarsa.
Domin alfarmar azumin Ramadan a wurin Allah, sai Ya kama Shaidanu Ya daure, bai bar su su yi tasiri a kan dan Adam ba. Don haka duk dan Adam din da ka gani a watan azumi yana aikata abin da ba Allah ne Ya ce ba, ba Annabi (SAW) ne ya ce ba, to kada ya zargi Shaidan a lokacin. Domin Allah Ya taimaka masa Ya kama Shaidan Ya daure, sai ya yi kokari ya taimaki kansa wajen inganta wannan tarbiyya. Abu na farko ke nan.
Sannan Allah (SWT) a lokacin azumi Yakan ninnka ladar aiki ga dan Adam bisa ganin damarSa. Kuma Ya kawo Daren Lailatul kadari a cikin wannan wata wanda ibada a cikinsa ya fi ibadar wata dubu. To malamai sun riskar da cewa haka ma na ranar, wato in ka hada ibadar rana da na dare ya fi na wata dubu, wato sama da shekara 83. Allah ne Ya ga dama Ya yi haka, ba don ibadar da mutum yake yi ta fi sauran ba ne. Sannan cikin falalarSa, cikin watan zai ’yanta mutane daga shiga wuta. Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda watan azumin Ramadan ya same shi, bai yi abin da za a ’yanta shi daga shiga wuta ba, in ya shiga wutar kada Allah Ya fito da shi.”
Komai garabasa ne a cikin watan Ramadan, duk abin da ka yi Allah zai ninka maka lada a cikinsa. Kuma tsayawa a yi ibadar ce za ta ba mutum damar inganta tarbiyyarsa a watan azumi.
Wani abin da nake so mu gane da za mu dabbaka darussan da azumi ke koyar da mu, a nan cikin garin Bauchi bisa karamin binciken da muka yi babu matalauci a cikin garin Bauchi da za mu ba shi zakka. Saboda mun yi nazarin masu wadatarmu a gefe daya da matalautanmu a gefe daya. Da masu wadatarmu za su dauki tarbiyya ta watan azumi su san cewa zakka dukiyar Allah ce a cikin dukiyarsu. Duk mutumin da dukiyarsa ta kai nisabi Naira dubu 600 da wani abu, to wajibi ne ya kasa 40 ya fitar wa Allah kashi daya. Dole ne, wannan kashi daya cikin 40 na Allah ne ba nasa ba ne.
To in kowa zai dauki kansa dan sanda na addini ba sai hukuma ta tasa shi a gaba ba, ya zauna a daki ya kasa dukiyarsa da ta shekara gida 40, ya cire daya na Allah. In ya ci wannan kashi daya ya san na Allah ne ya gurbata sauran dukiyar, Allah Ya cire albarka a cikinsu, kuma Ya daina kallonsu, Ranar Lahira zai mayar da su wuta na musamman wanda Hadisin da ya siffanta dukiyar wanda bai fidda zakka ba, Hadisin ya fi kowane ban tsoro a cikin Hadisan da ake karantawa. To da kowa zai zama dan sandan kansa ya fitar da zakka zai zamo ba mu da matalauci a Bauchi. Domin kowane mutum zai mallaki abin da ya kai nisabi, sai dai ya saurari wata shekara ya fitar.
Ashe rashin tarbiyya ko aiki da tarbiyyar da azumi yake koyarwa na mutum ya zama dan sandan kansa wajen kiyaye dokokin Allah ne ya sa ake samun matalauta a tsakaninmu.
**{Legacy activities, comments etc counter: 534; topic series: 5; forum: MediaHausa; associated: 5- /*}