Labarai da Ra'ayi
Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi

Koma zuwa "Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi"

Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi
MediaHausa
Site Admin
Masu rubutu: 121
An haɗa: Talata Oct 21, 2025 9:40 am
Lambobi:

     MediaHausa Site Admin    Masu rubutu: 121    An haɗa: Talata Oct 21, 2025 9:40 am    Lambobi:   


Buga by MediaHausa »

Esin127 *Legacy Post Number 105 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (12)
Timeline: 2012-10-14 21:54:52


Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (12)

Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah

Akwai kura-kuran da ake aikatawa da ya kamata a nisance su:

1. kin kwana a Muzdalifa ba tare da larura ba.Maganar da ake yi cewa ba wajibi ba ne a kwana a Muzdalifa bisa koyarwar Mazhabar Malikiyya, ba haka ba ne. Domin abin da ya tabbata a Hadisin Manzon Allah (SAW0 da aikin magabatan kwarai shi ne Mazahabin Imam Malik. Kuma da’awar cewa ana sauka a Muzdalifa gwargwadon yin shafa’i da wuturi, bayan Sallar Issha, wannan na nufin masu uzuri ne kawai, amma ba wadanda ba su da wani uzuri ba. Masu uzurin ma, sai dare ya raba, kamar yadda Hadisi ya tabbatar.

2. Wucewa Mina a yi jifa da dare kafin ketowar alfijir, wannan shi ma kuskure ne, domin ba a yin jifa a wannan daren, sai bayan alfijir ya keto. Saboda haka masu yin haka ba su da wani dalilin da suka dogara da shi a kan haka. Kuma ana ji wa irin wadannan mutane tsoron kada aikinsu ya tafi a banza. Allah Ya kiyashe mu, kuma Ya ba mu ikon ji da aiki da shi.

3. Wasu mahajjatan suna wucewa Makka su yi dawaful Ifada a cikin daren, sannan idan gari ya waye suna yin Sallar Idi tare da mutanen Makka, wannan shi ma kuskure ne. Saboda shi dawaful Ifada ba a fara yin sa sai Ranar Idi, kuma Ranar Idi tana farawa ne bayan alfijir ya keto a ranar goma ga watan Zul-Hajji. Kuma shi mahajjaci ba a kallafa masa halartar Sallar Idi ba.

Tambaya ta 37: Wadanne irin ayyuka ake yi a Ranar Idi, bayan an bar Muzdalifa zuwa Mina?

Amsa: 1. Jifar Jamra Babba (Al-Akaba) wadda mun riga mun yi cikakken bayanin yadda ake yin ta a baya. 2. Daga nan, sai mahajjaci ya je ya yi yanka, kuma an fi son Alhaji ya yanka dabbarsa da kansa. Idan bai samu dama ba, sai ya wakilta wani amintacce ya yanka a maimakonsa. Ana son ya ci wani abu daga cikin naman hadayar ya sha romon, idan ya samu dama. Sannan, ana so a yayin yankan ya ce: “Bismillahi wallahu Akbar Allahumma inna haza minka walaka, Allahumma takabbal minni.”
Ma’ana: “Da sunan Allah, kuma Allah ne Mafi girma. Ya Allah wannan (dabbar hadayar) daga gare Ka take, kuma a gare Ka za ta koma. Ya Allah Ka karbi wannan ibada daga gare ni.”

Idan Mahajjaci bai samu damar yanka ba a ranar Idi, to dukan ranakun Mina, ranakun yanka ne. Domin Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk ranakun tashrik (wato ranakun Mina) ranakun yanka ne.” Silsilah As-Sahiha: Hadisi na 2476.

Wanda ya yi hajjin kirani ko Tamattu’I shi ne kawai hadaya ta wajaba a gare shi, amma idan mai Ifradi ya yi yanka, to, ya yi tadawwu’i (nafila) ne kawai, don yanka hadaya bai wajaba a kansa ba. kamar yadda bayani ya gabata a can baya. Sai dai mai kirani ko mai Tamattu’in da bai samu ikon yin yanka ba, to, zai yi azumi na kwana uku a cikin kwanakin Hajji, kuma ya yi bakwai idan ya dawo gida.

3. Bayan yanka, sai a yi aski. Maza ne kawai ke yin aski, mata kuwa za su datsi kadan ne daga gashin kansu gwargwadon tsayin dan yatsa. Sai dai yin aski ga maza shi ne ya fi, domin Manzon Allah (SAW) ya kwadaitar da yin hakan. Idan ba a samu dama ba, sai a yi saisaye.

4. Daga nan, mahajjaci zai cire haraminsa, idan bai samu dama ba kuma ya bar shi a jikinsa har sai ya gama dawaful Ifada.

Lallai ne mahajjaci ya fahimci cewa ba a yanka hadaya, ba tare da an yi aski ba. Aski kuwa ba a yin sa sai Ranar Idi, bayan an yi jifa. Wannan shi ne abin da nassin Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah (SAW) da aikin magabata na kwarai suka tabbatar. Ubangiji (SWT) Ya ce: “… kuma kada ku aske kawunanku har
sai hadaya ta isa wurinta (watau Mina a Ranar Idi)” (Bakara: 196).

Kuma sanannen abu ne cewa Manzon Allah (SAW) shi ne mai fassara mana Alkur’ani; shi kuwa bai yi yanka ba, har sai Ranar Idi, haka ne kuma sahabbansa suka aikata a bayansa. Don haka, kada mahajjaci ya kuskura ya yanka hadayarsa kafin Ranar Idi, kamar yadda wadansu suke yi.

Koda yake akwai wadanda suke dogaro da maganar Imam Munziri a cikin Mukhtasar Khalil cewa, za a iya yanka hadaya kafin Ranar sallah. To hakika wannan maganar ko a mazahabarmu ta Malikiyya, ba ta da rinjaye. Haka kuma, wadanda ke kafa hujja da Hadisin da aka tambayi Manzon Allah (SAW) a Ranar Idi kan gabatar da wasu ayyukan kafin wasu, kamar gabatar da aski kafin yanka, ko gabatar da dawafi da Sa’ayi kafin aski, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “ai babu komai.” To, dogaro da wannan Hadisin wurin yin yanka kafin Ranar Idi kuskure ne. Domin wadannan ayyuka da Manzon Allah (SAW) ya yi rangwame a kansu, dukkansu ayyuka ne na Ranar Idi, illa iyaka an gabatar da wasu ne a kan wasu, amma yanka hadaya kafin Ranar Idi sabanin Sunnar Manzon Allah (SAW) ne. Saboda haka, a yi hattara wurin saba wa umarni da ayyukan Manzon Allah (SAW).

Amma za a iya yanka fidiya (wato dabbar da mahajjaci ke yankawa domin wata larura ko rashin lafiya da ta sanya ya aikata wani abin da aka hana shi aikatawa. Misali kamar mutumin da ya yi aski saboda wata rashin lafiya a kansa da sauransu). Domin Hadisi ya tabbata cewa wani sahabin da yake fama da larurar kwarkwata a kansa, sai Manzon Allah (SAW) ya umarce shi ya aske kansa, sannan ya yanka fidiya, amma ba tare da ya kayyade masa rana ko wuri ba.

5. Bayan an yi aski, sai a je a yi dawaful Ifada, wanda yake shi ma rukuni ne daga cikin rukunan aikin Hajji. Mai yin Hajjin Tamattu’i zai yi Sa’ayin Safa da Marwa bayan ya yi dawaful Ifada. Amma idan ba a samu damar yin dawaful Ifada a Ranar Idi ba, to, sai a sake mayar da harami har zuwa ranar da za a samu damar yin dawafin. Kuma za a iya yin dawafin tun daga wannan ranar har zuwa karshen kwanakin Mina. Domin Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika wannan ranar rangwame ce a gare ku: idan kun yi jifar Jamrah komai ya halatta a gare ku, ban da mata. Idan kuka yi yammaci kafin ku yi dawafin wannan daki (dawaful Ifadah), ba ku samu yin dawafin wannan dakin ba, (watau har rana ta fadi), haramci ya sake komawa gare ku kamar yadda kuke da farko kafin ku yi jifar Jamrah, har sai kun yi dawafin (Ifadah). A duba Sunan Abu Dawud: Kitabul Manasiki, Babul Ifadati Fil Hajji, Hadisi na 1999.

Ma’ana za a sake mayar da harami har sai an yi dawaful Ifadah.

Tambaya ta 38: Alhajin da ya je yin dawaful Ifadah Ranar Babbar Sallah bai samu dawowa Mina ba har rana ta fadi, shin akwai yanka a kansa?

Amsa: Alhajin da ya samu kansa a irin wannan hali ba komai a kansa koda dawafinsa da sa’ayinsa sun hana shi komawa da wuri ko wasu bukatunsa sun kai shi har zuwa dare. Abin nema a gare shi idan ya gama, komai dare, ya koma Mina ya kwana a can. To amma abin bakin ciki akwai wasu malamai suna bada fatawa cewa akwai yanka a kan duk Alhajin da rana ta fadi yana Makka bai koma Mina ba, ba tare da wani dalili mai karfi wanda suka dogara a kansa ba. Muna yi musu nasiha su ji tsoron Ubangiji (SAW) a kan irin wadannan fatawoyi.


**{Legacy activities, comments etc counter: 616; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}

Aika amsa

Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (12)



Bayar da Amsa

Koma zuwa "Labarai, Makaloli da Ra'ayoyi"

Bayar da Amsa