Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (7)
An buga: Litini Feb 09, 2026 2:18 am
*Legacy Post Number 98 from MediaHausa
Topic: Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (7)
Timeline: 2012-10-14 21:36:07
Fatawoyin Aikin Hajji da Umara da Ziyara (7)
Daga Sheikh Abdulwahhab Abdullah
11. Tambaya: Shin ko mace mai takaba ko idda za ta iya zuwa aikin Hajji?
Amsa: A'a, bai halasta ba ga mace mai idda ko takaba ta tafi aikin Hajji, domin Shari'a ta umurce ta da lazimtar dakinta. Saboda haka, ba za ta fita ba, sai da larurar da Shari’a ta yarda da ita (kamar zuwa asibiti don neman magani, yin sana’a i... dan babu wanda ke daukar nauyinta, ko ziyarar iyaye da `yan’uwa).
Dalili kuwa shi ne abinda ya tabbata cewa Sayyadina Umar bn Khaddab da Uthman bn Affan (Allah Ya yarda da su) suna mayar da mata wadanda suka yi nufin tafiya Hajji, alhali suna cikin takaba, daga wurin da ake kira Baidaa. , (don su koma) Madina. Haka nan, a cikin tabi’ai, Sa’idu bn Musayyib ya bada fatawa da haka.
Amma akwai magana ta biyu da ake dangana ta ga Sayyidina Aliyu da Ibn Abbas da Jabir bn Abdullah da A’isha (Allah Ya yarda da su) cewa mai takaba ko idda za ta iya tafiya aikin Hajji ko Umrah. Har ma an samu cewa Nana A’isha ta fita zuwa Umrah tare da Kanwarta Ummu Kulthum, wadda ke yin takaba.
Shi kuwa Kasim bn Muhammad ya ce: "Mafi yawan sahabbai sun yi wa A’isha inkari a kan wannan. Ibn Abdul-Barri ma ya bayyana cewa mafi yawancin malaman zamaninta sun yi mata inkari. Ya Kara da cewa: "Magana mafi rinjaye ita ce fatawar Umar da Uthman da Sa’idu bn Musayyib (Allah Ya yarda da su), kuma ita ce muka rinjayar."
Amma malamai sun ce idan ta fita zuwa aikin Hajji ko Umrah, sai ta samu labarin mutuwar mijinta, alhali tana kusa da gari (kamar filin jirgi a nan Nijeriya), to sai ta dawo. Idan kuwa ta yi nisa, sai ta ci gaba da aikin Hajjinta ko Umrah.
12. Tambaya: Yaushe ne maniyyaci zai dauki niyyar aikin Hajji, kuma a ina zai dauka?
Amsa: Maniyyaci zai yi niyya ne a miKati yayinda ya daura ihraminsa,kuma zai Kudurta niyyarsa ne tare da talbiyya. Amma ba zai furta lafazin niyyar ba. Hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Umar (Allah Ya yarda da su) cewa Manzon Allah ...
(Sallallahu alaihi Wasallam) ya kasance idan ya daidaita a kan abin hawansa, bayan ya kammala nafila a masallacin Zul Hulaifah, yana daga murya da talbiyya.
A wannan lokacin ne zai yanke niyyar irin nau'in Hajjin da zai yi azuciyarsa.
13. Tambaya: Menene ma’anar talbiyya?
Amsa: Da farko ga yadda lafazin talbiyya ya ke:
لبيك اللهم لبيك لبيك لآ شر يك لك لبيك , إ ن الحمد و النعمة لك والملك لآ شريك لك
Malamai na da fahimta dabam-daban dangane da ma’anar wannan lafazi, kamar haka:
· Wasu malamai sun ce ma’anar talbiyya shi ne: "Na yi nufin zuwa gareKa ya Allah, na yi nufinKa, kuma na fuskanceKa ya Allah."
· Wadansu malaman kuma suka ce ma’anar talbiyya shi ne: "Soyayya ta zuwa gareKa ya Allah"
· Amma ma fi rinjayen malamai sun tafi a kancewa ma’anar talbiyya shi ne: "Amsa kira zuwa gareKa ya Allah, kuma ni mai tsayuwa ne a kan bautarKa, baKa da abokin tarayya. HaKiKa dukan godiya da girmamawa da ni’ima sun tabbata a gareKa. Mulki kuma ya tabbata a gareKa, ba Ka da abokin tarayya."
**{Legacy activities, comments etc counter: 627; topic series: 2; forum: MediaHausa; associated: 2- /*}